A ranar ta farko ta ziyarar da ma'aikatan diflomasiyya ke yi a lardin Jiangsu na kasar Sin, a yau sun kai ziyara sassa daban daban na birnin Nanjing, babban birnin lardin na Jiangsu, ciki har da katangar tsohon garin Nanjing da aka gina shekaru sama da 600 da suka wuce da kogin Qinhuai da ya ratsa birnin. Baya ga haka, sun Kalla tare da gwada al'adar hada shayi ta Sinawa. Mr. Sidibe Mohamadou Aboubakar daya daga cikin wadanda suka amdsa goron gayyatar wannan ziyara kana jami'in watsa labarai na ofishin jakadancin jamhuriyar Nijer a nan kasar Sin ya ce, tarihi da al'adun birnin ya burge shi kwarai da gaske, kuma abin jinjinawa ne yadda aka adana tarihi da al'adun gargajiya yadda ya kamata. A cewarsa, wanda bai san tarihinsa, bai san inda ya fito da kuma inda za shi ba.(Lubabatu)