



A ci gaban ziyarar jami'an diplomasiyya a jardin Jiangsu na kasar Sin, jami'an diplomasiyya daga kasashe bakwai, ciki har da jami'in kula da harkokin labarai a ofishin jakadancin jamhuriyar Nijer da ke nan kasar Sin, Mr.Sidibe Mohamadou Aboubakar tare da uwargidansa, sun kai ziyara birnin Zhenjiang, inda suka ziyarci kauyen Qianhua da ke da dadadden tarihi da ke tsaunin Baohua.
Tsaunin Baohua shi ne inda shahararren kogin nan na Qinhuai na lardin Jiangsu ya fara, kuma kauyen nan na Qianhua da aka ziyarta ya nuna irin yanayin al'adu da zaman al'umma na Sinawa a lokacin daulolin gargajiya na Ming da Qing.(Lubabatu)